YADDA AKE SHAGWABA
Matan yanzu an sansu da son yima samarai shagwaɓa musamman in saurayin yazamo mai san budurwan sosai. Akwai hanyoyi da dama wacce zaki iya yi masa hakan a sauwake tare da bashi nishadi.
Yana da matuƙar amfani kisan dai dai lokacin da yake farin ciki soboda hakan zai kara shaƙuwa a tsakaninku. Domin sanin yadda ake ma saurayi shagwaɓa don sa shi farin ciki, ki karanta wannan rubutun nawa taƙaitacce.
Karanta: YADDA AKE RAGE SHA'AWA
Menene Shagwaɓa A Soyayya
Shagwaɓa a soyayya yanada matuƙar amfani sosai dan yana kara shaƙuwa da farin ciki tsakanin masoya biyu. Shagwaɓa a soyayya yana nufin yin abubuwa tare tsakanin masoya dan kara shaƙuwar soyayyar su. Hakan yana yuwa ta hanyar yin wasu abubuwa wanda zai sa shi saurayin ya ga dace war kula da ita sosai.
Karanta: ALAMOMIN SOYAYYAR GASKIYA
In a soyayya akwai shagwaɓa tsakanin masoya, to koda ace masoyan na jin kunyan guna, shagwaɓa dake tsakaninsu zai sa har su iya gayawa juna sirrinkansu a sauwaƙe. Kuma mafi yawancin mata a yanzu suna yawan yi ma samaran su shagwaɓa dan su gane irin san da yake masu, kuma suna samun nasarar sanin hakan.
Abin ban sha'awa game da shagwaɓa shine inka san wata baka san wata ba. Mata suna da salo da ban da ban na yin shagwaɓa ga samaran su a kowani lokaci. Yanzu ma in mace nasan abu wajen saurayin ta, kafin ma tasamu abun a wasu lokutan, sai ta mai shagwaɓa kafin zai iya bata wannan abun batare da yasan yana badawa ba.
Karanta: HALAYEN MATA WANDA MAZA BASA SO
Wasu mazan ma gani suke in budurwa bata ma saurayin ta shagwaɓa, hakan na nuna cewa bata son shi ko kadan. In akwai shagwaɓa, toh akwai yarda da juna sa'anan kuma akwai nishadi da farin ciki. Mafi yawanci in saurayi na cikin damuwa ko ɓacin rai, shagwaɓa daga wajen abun ƙaunar sa na iya kau da wannan halin ba daya ke ciki.
Soboda haka, shagwaɓa a soyayya na da matuƙar amfani a rayuwar masoya.
Karanta: ABUBUWAN-DA-MAZA-KE-SO-JIKIN-MATA
ANFANIN SHAGWAƁAR BUDURWA GA SAURAYIN TA
Me ya sa muke da gaske game da rashin zama da gaske? Dalili ɗaya shi ne, dariya yana da daɗi, kuma dariya tare da wani ya ma fi daɗi. Muna so mu kasance tare da mutanen da za su iya sa mu dariya, musamman ma idan za su iya taimaka mana mu yi dariya game da abubuwa da yanayin da ke sa mu damuwa.
Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA
Amma akwai hanyoyi da yawa don jin daɗin rayuwa. Me ya sa mutane ke daraja abin dariya fiye da, a ce, zama ƙwararren mai dafa abinci ko mallakar gidan bakin teku? Shagwaɓa namiji yana ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin ƙarfafa dangantakar ku. Don kawai kun kasance tare da juna sama da shekara ɗaya ko biyu, hakan ba yana nufin ba za ku iya yin shagwaɓa ba a cikin soyayya da aminanku ba.
Koyaushe kuna iya ba da shi ta hanyoyi daban-daban. Wannan zai taimaka muku wajen kiyaye walƙiya a cikin dangantakar ku. Shagwaɓar budurwa ga saurayin ta yana da matuƙar anfani sosai a gudanar da soyayya, musamman ma a wannan zamanin.
Karanta: YADDA ZAKA SAKA BUDURWA TA KWARE MAKA
Ita shagwaɓar mace a soyayya, abu ne wanda yake kamar sanadari, domin yin ta a soyayya ba don jindaɗi bane kawai tsakanin masoya ba face tana taimakawa wajen kara ƙarkon ita kanta soyayyar. Shagwaɓa a ko ina yana da matuƙar anfani. Haka zalika shagwaɓar mace ko shagwaɓar budurwa ma takan haifar da wasu halaye.
Waɗannan kyakyawar halayen sune nuna gazawa, girmamawa tsakanin mutane masoya, rarrashi, tana nuna ban gajiya, har ila yau tana sanyaya rai. Dukkan waɗannan abubuwane dake da tasihi sosai ba kaɗan ba wajen kara cusa soyayya a zuciyan saurayi.
Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA
Daga cikin anfanin shagwaɓar budurwa ga saurayin ta , akwai abubuwa kamar haka:
- shagwaɓar mace na sanya zuciyan saurayi ya narke, yaji babu abunda yake son ya gani sai masoyiyansa na hakiƙa. domin zai ɗauki shagwaɓar da anfani sosai.
- Shagwaɓar budurwa yakan kara limar ko shigar da zuciyan saurayin ta a duk lokaci da hankalin sa ya tuna masa da ita sai yaji wani daɗi a ran sa
- shagwaɓar budurwa har ila yau tana taimakawa yayin samar da amincewa tsakanin masoya. Sanadiyar shagwaɓar, sai suji sun yarda da kansu sosai.
- Anfanin shagwaɓar mace ga saurayinta ta da akwai kauda zargi. Idan soyayya ta kasance akwai shagwaɓa sosai daga ɓangaren budurwa, yana kau da tunanin saurayin daga zargin budurwar tana wani abun da bai kamata ba a cikin soyayyar su.
- shagwaɓar mace tana haifar da gaskiya, amana, kawaici, yarda, nuna soyayyat ta hakiƙa, sadaukar da rai ko jiki, zaman daɗi ko kunshi, da kuma rashin son kai.
- Ita shagwaɓar budurwa tana sanya kusanci tsakanin ta da saurayin. A ƙullun shi saurayin yana son ya ga masoyiyansa tare da shi. Zai ji ba daɗi idan babu ita a kusa da shi.
Karanta: YADDA-AKE-GANE-MATAN-AURE-MASU-BIN-MAZA
Salon Shagwaɓa: Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaɓa
Bayan sanin amfanin shagwaɓa da mecece ita, yanzu kuma zamu duba yadda ake yin shagwaɓar wato salon shagwaɓa a soyayya. Akwai hanyoyi da dama da mace zata iya ma saurayin ta shagwaɓa amma a wannan taƙaitaccen rubutun nawa, zaku ga salon shagwaɓa a soyayya guda sha daya (11).
1. Kibashi Suna Mai Ban Dariya
Maza na matuƙar son suga budurwa ta kira su da wata suna daban wacce basu taɓa kiran su da ita ba. Wannan salon shagwaɓar yafi aiki a sanda kike son saurayin ki yama ki abunda kike ganin zaiyi matuƙar wuya a wajen shi.
Karanta: YADDA AKE YIN SHAGWABA
In kika kira saurayin ki da suna na ban dariya, hakan zai sa dukan ku farin ciki har ma yayi maki abu fiye da yadda kike tinanin zaiyi. Soboda haka yana da matuƙar amfani kisan yadda ake ma saurayi shagwaɓa.
Kafin hakan, ki kwantar da hankalin ki sosai kisan irin abubuwan dayake so, daga nan ne zakiyi iya sanin sunan da zaki sa mashi. Misali in mutun ne mai san kwallo, sai ki kira shi da sunan dan kwallon da yafi so, daga nan sai kinuna mai kina kishi da hakan a shagwaɓe.
Karanta: ILOLIN-AUREN-WACCE-BATA-SONKA
2. Ki Ɗauki Hoto Mai Ban Dariya Ki Nuna Mai
Ɗaukar hoto mai ban dariya ki nuna wa saurayin ki musamman inya bukaci kituro mai hotonki ita ma wata salon shagwaɓar ce wanda ke kara shaƙuwa tsakanin masoya. In yadda ake ma saurayi shagwaɓa shine muradinki ta fari, ki bi wannan hanyar mai sauki.
In ya ga hotarki mai ban dariya, hakan zai sa shi yafara maki dariya kuma hakan zai sa shi cikin farin ciki musamman in kintabeyi shi in hoton yayi kyau, komai ya fada a wannan lokacin zai sa ki gane matsayin ki a wurin shi. In ma kin nuna mai ɓacin rai, kinga sai lallaɓe ki kamar kwai tin da farin cikin ki ita ce muradin sa a koda yaushe.
Karanta: GASKIYAR BAYANI AKAN FATALWA
3. Ki Zama Mai Yawan Mai Bazata
Ga sirri gareku yan mata, in kinason sanin halin saurayin ki, kizama mai yawan mai bazata. Kamar fito ina angwuwar ku, gani a kofar gidan ku. Idan akwai abun da yake ɓoye maki to ba zai fito ba. Amma in ya fito, mai gaskiya ne shi.
Yin ma saurayin ki bazata wata salon shagwaɓar ce wanda zaki gane in saurayin ki ya dace ko kuma bai dace dake ba. So budurwa ta tai na saurayin ta tambaya amma sai yayi maki ƙaruwa, bazata ita ce hanya mafi sauki ta gasgata maganar sa. Amma kuma in hakan zaki, yana da kyau kisan yadda zaki kula da al'amari.
Wannan wata hanya ce ta koyan yadda ake ma saurayi shagwaɓa mai sauki ga mace mai wayau da kula.
Karanta: YADDA-AKE-MALLAKE-YAR-MASU-KUDI
4. Ki Ɗauki Abubuwa Masu Mahimmanci Kamar Basu Da Shi
Yan mata adon gari, farin cikin ku muradin samaran ku, ɓacin rai ku damuwa ce. Wata salon shagwaɓa ce ɗaukar abubuwa masu mahimmanci kamar basu da ita. Nuna shagwaɓa ta wannan tsigar nasa ki gane matsayin ki a wajen masoyinki.
Indai yana son ki har zuciyar sa, ko me kika yi a wurin shi ita ce dai dai. Misali ace zaku fita shopping ko wajen shakatawa yace maki karfe 3 za'a he, sai yazo karfe 3 kice masa kwalliya ya bari sai karfe 4, kinga shagwaɓar tasa makwulkin soyayyar ta dawo hannun ki sai yadda kika juya shi.
Dama mulki a soyayya, budurwa aka sani a matsayin sarauniya kuma komai suka yanke, ya zauna.
Karanta: YADDA ZAKA MALLAKE BUDURWAR KA
5. Kisa Yafara Yaƙin Kaska Alokacin Da Bai So
In kina tare da saurayin ki, abubuwa waɗanɗa zai kara kusanci a tsakaninku su be abubuwan da zaku ringa mai. Wata salon shagwaɓar ce fara masa sa wasa ta yaƙin kaska.
Wata lokacin zaki ga kuna magana da saurayin ki amma kiga magana ta ƙare a bakin sa ya rasa mai zai fada, kema haka din kin rasa abun cewa. Zaku iya samun abun magana akai in yaƙin kaska tashigo tsakaninku. In hakan ta faru, zaki iya kawo wata maganar sa zai sa ku fara gardama.
Bai da wani zaɓi da yabi abun da kika zaɓa. Zaki iya ɗaukan abu kisa mai a gefen kunni ko kuma a saman hula kice ba ke kika yi hakan ba. A zahiran ce ya san kece, amma soboda yasan shagwaɓa kike yi masa sai yace maki ya yarda da hakan. Hakan na da matuƙar nishaɗantuwa.
Karanta: KALAN MAZAN DAKE WAHALAR DA MATA
6. Ki Ringa Masa Wasa Da Abinci
A wasu lokutan in kun fita wajen cin abinci, zaki ga mafi yawanci shi zai riƙa sa maki abincin a baki, amma a zuciyar sa shi ma yana son hakan. In kika ɗibo abincin zaki sa mai a baki, da zaran ya buɗe bakin sai kiyi maza ki dauke chokalin ki cinye kuna kisa shi yasa maki a baki.
Sai dai kuma ba dukkan maza ake ma shagwaɓa ta wannan tsigar ba, sai dai in mace ce wacce ta san hannun ta sosai.
7. Ki Sa Ya Biyo Ki Ta Hanyar Ɗaukar Abun Sa
Zaki iya yi ma saurayin ki shagwaɓa ta hanyar ɗaukan masu abu kamar in kun fita shakatawa ko dai kuna tare a waje na masoya. In kina so kuɗanyi wasa amma yaƙin, sai kidau wani abu nasa kisa shi ya taso har yabi ki.
Da kinyi gudu kadan sai ki ce masa kafafuwan ki da hannayen ki na maki ciwo. Kinga yasan ba da gaske bane, amma zai fada maki kalamai masu ɗaɗi dasu faranta maki rai kawai dan yaga kina cikin farin ciki in kuna tare.
Karanta: YADDA AKE HIRAR SOYAYYA FARKON HAƊUWA
8. Ki Katse Shi Ayayin Da Hankalinsa Bai Tare Da Ke
Mafi yawancin lokutan, zaki ga saurayi yaje gurin budurwa amma sai kiga hankalin sa ba ya tare da ita kuma hakan na matuƙar ɓata ta rai. In saurayin ki maki hakan, ta hanyar shagwaɓa ce kawai zaki iya karkato tinanin sa.
Misali ki fara masa kuka (amma fa na wasa) kinga ay zai fara lallasan ki yana tambayan ki meyasa ki kuka, a hakan kinyi nasarar karkato da tinanin sa gare ki.
Karanta: YADDA-AKE-CHATTING-DA-BUDURWA
9. Ki Zama Budurwa Mai Kishi
Ana yawan cewa mata sunfi maza kishi, amma gaskiyar magana itace maza sunfi mata kishi sai dai su basu cika nuna basu a fili ba. Maza na matuƙar son su ga budurwar su tana nuna kishi akan su, kuna suna kiran hakan da shagwaɓa.
10. Nuna Halinki Na Musamman
Mafi yawancin lokutan, saurayi sai ya ringa cewa yafi budurwa shi wani abun, kuma hakan baya masu ɗaɗi. Amma daga sanda suka nuna maka irin da baka santa, sai kaji shi yana cewa ashe dama wacce ta iya shagwaɓa haka.
Karanta: MATA-DA-MAZAN-DA-SUKA-CANCANCI-AURE
Misali kamar ace kullin sai yace kin cika yi kamar yar kauye amma kuma hakan wasa ce a wurin shi, sai kiyi masa hali irin na ƙauya wan yagane cewa ke ɗin ta da ban ce. Ki nuna mai Ubangijin da ya halicce ki ya baki baiwa ya yin abubuwa daban daban a lokuta daban.
11. Yin Mai Magana Da Lafazin Waje
In kina ma saurayin ki magana da lafazin waje, hakan na janyo farin ciki da nishaɗi in kuna tare. Kinga in kika fara magana ta lafazin waje dariya ze fara maki yace baki iya ba.
Kuma sai ki ce masa kinyi magana dan yace kin iya kuma shi ne zai ce baki iya ba. Sai yayi murmushi ya kalleki ya fara maki ɗaɗin baki. Hakan na yuwa ne kawai in shagwaɓa ya shiga tsakanin masoya biyu
Yadda Ake Shagwaɓa a Waya
Ita shagwaɓa a waya wato wani haline ko kuma ɗabia wanda a shawarce, yakamata masoya su zamto sun iya sosai. Domin an shaida itama tana cikin ire-iren abubuwan dake ainufin janyo hankalin masoya. Sai dai kuma ana son a ƙullun a ringa lura ko kuma kulawa da halin masoyin ko masoyiyan da kuma lokacin da yake ko take cikin jindaɗi na nishadi.
Karanta: AMFANIN AUREN BAZAWARA KO WACCE TA GIRMEKA
Ta ko wani hanya ko dalili, kar a tadda wanda ake so da soyayya cikin ɓacin rai a kama yin masa shagwaɓa, Hakan ba zai taɓa burgeshiba ko kaɗan. Sai an bari ana cikin nishaɗi ko kuma cikin hutawa, sai a dameshi da kira, ta hanyar tura saƙo ta waya ana nuna masa kamar za'a yi kuka tamkar karamin yaro, ko kuma dai ko wani sauran yadda ake shagwaɓa a waya irin ta zamani.
Yin amfani da lokaci tare da saurayi a cikin mutum yana da kyau, amma akwai iya zuwa ranar da za ku ciyar da ɗan lokaci. Alhamdulillahi, shagwaɓa a waya hanya ce mai kyau don ci gaba da kasancewa tare da shi a kullum. Mun tattara wasu kyawawan abubuwan shagwaɓa a waya da zaku iya yi wa masoyan ku don sa shi murmushi ya kuma kara kewarsa.
Karanta: YADDA AKE ZUWA WA AMARYA DAREN FARKO
1. Tura masa saƙon da sassafen safiya
Zai zama abu na farko da zai ko zata gani idan aka farka. Yana da kyau koyaushe ka tashi zuwa rubutu daga masoyi! Lokacin da kuka tashi daga gadon barci, ayi sauri a aika masa da safiya don yin ranarsa.
Gwada wani abu kamar: “Barka da safiya! Ina fatan kana da babbar rana." “Lokacin tashi! Na ƙosa na ganka" “Barka da safiya hasken zuciya! A ci gaba da tafiyar da hirarka ta hanyar aika masa da wasu tambayoyi. Kuna iya tambayarsa game da dangantakar ku, inda yake ganin kansa a nan gaba, ko kuma kawai abin da yake ciki a yanzu.
Karanta: ALAMOMIN-SOYAYYAR-GASKIYA
Yawan tambayoyin da kuke yi, ƙarin jin daɗin tattaunawar ku za ta kasance.
2. Yi masa kwarkwasa
Aika saƙon rubutu mai ban sha'awa don samun injinsa ya tafi. Domin ba ku tare a cikin mutum ba yana nufin ba za ku iya kwarkwasa ba! Yi aikin jin daɗi, saƙo mai ban sha'awa don aika masa, kamar: "Na yi mafarki game da kai a daren jiya.
Kana son jin me ke ciki?" "Idan muka makale tare a tsibirin da ba kowa, menene farkon abin da za ka yi?" "Ina tunanin ka da yarda ka tsunbace ni jiya, Inama ace kana nan".
Karanta: ALAMOMIN KAMUWA DA SOYAYYA
3. A tambaye shi/ta a aika mafi kyawun hoto da aka taɓa ɗauka
Yana iya zama na kansa, dabbobinsa, yanayi-komai! hakan ma shagwaɓa a waya ne. Nemi a aiko da hoton fasaha don a iya ba da labarin yadda ya yi kyau. A biyoshi da mafi kyawun hoton da kuka taɓa ɗauka domin ku duka ku yaba wa juna. A sanar da hakan ta hanyar faɗin wani abu kamar, “Mene ne mafi kyawun hoto da ka/ki da shi akan wayar?
Karanta: AMFANIN-NONON-AKUYA-GUDA-8-JIKIN-MUTUM
4. Yi Masa Yabo
Yi shagwaɓa a waya ta hanyar Nuna kamanninsa, halayensa, ko ma muryarsa. A aika masa da rubutu yana ana shi yabo don ya san ba za'a iya jira a sake ganinsa ba. Idan ba ku da tabbacin abin da za ku faɗa, yi tunanin abin da aka fi so game da shi. Gwada wani abu kamar: "Muryar ka ita ce sautin da na fi so." "kayi yi kyau sosai a wannan hoton da ka buga a baya." “Ina jin lafiya a kusa da kai.
5.Yi Masa Shagwaɓa A Waya Ta Kira
A lura da tsarin aikinsa, idan baya wani aiki, a ringa damunsa da kira. A ƙullun ya ga ana yawan kiransa. shagwaɓa a waya ta hanyar yawan kira zai nuna masa cewan an damu da shi kuma ana tunanin sa a ko wani lokaci.
Karanta: YADDA-AKE-CHATTING-DA-BUDURWA
Kalaman Shagwaɓa a Soyayya Masu Daɗi
Yawancin mutane ba su gane cewa mafi mahimmancin ɓangaren dangantakarku shine kiyaye mahimman masoyan su da kuma sasu farin ciki ba. Da wannan tunanin, faranta wa masoyi ko masoyiya rai ta hanyar kalaman shagwaɓa shine abu na farko da yakamata ya kasance a zuciyar ku don ƙirƙirar alaƙa mai ni'ima.
Mata da Maza suna son a yi musu shagwaɓa. Dukanmu mun san cewa maza da mata suna son shagwaɓa daban-daban. Amma ko ta yaya suka sa kansu su bayyana, maza ko mata suna son a yi musu shagwaɓar.
Kuma wace hanya ce mafi kyau don shagwaɓar da wanda ake so da soyayya fiye da aika masa da kalaman shagwaɓa masu kyau duk tsawon rana! Anan akwai irin waɗannan kalaman shagwaɓa guda 11 don aika wa Masoyi ko masoyiya.
Rike hannaye, satar sumba, juyi a gado… wannan ke nan a raina na karshen mako.mai zai hana ka zo mu fara.
Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA
Ya kake ganin zuwa gidanmu anjima na yi maka abincin dare mai ban sha'awa. Kuma za mu iya Netflix da kuma shakatawa daga baya?
Strawberry ko cakulan… menene ke zuciyar ka , habibiy?
Nasan dole ne ka gaji a wurin aiki. Ya kake ganin yin pedicure ga yarima na?
Rungumar beyar tana jiran ka lokacin da zaka isa gida daga wurin Aiki!
Na yi shirin kawo maka kayan kari a kan gado a ranar Jumma'a mai zuwa. Mu sanya daren Asabar mai ban mamaki!
Sannu kyakyawa, ina zuwa da jakar soyayya da runguma. kofarka ta kasance a bude.
Ina son yin tunani game da duk hanyoyin da zan so ka a nan gaba. Daren yau ba mummunan lokacin farawa ba ne.
Ba Kia ganin ya kamata muyi wasa a daren yau? idan ka yi nasara, zan lalatar da kai da kyaututtuka, idan kuma ka rasa, ka lalatar da ni!
Ba zan taɓa iya daina yabon kyawun ka ba!
Na koya maka wasu dabarun tausa. Za su yi abubuwan al'ajabi don gajiyarka!
Karanta: ABUNDA AKE NUFI DA CUTAR SANYIN GABA DA HANYOYIN MAGANCE SU
Daga karshe
Bincike da yawa da dama sun nuna cewan iyaye da ma mutanen gida sun fi son yara masu shagwaɓa domin ita shagwaɓa tana haifar da wasu halaye masu matuƙar anfani wajen zamantakewar mutane. Musamman ma shagwaɓar budurwa ga saurayin ta. Don haka, ya kamata masoya mata su ɗauki yadda ake ma saurayi shagwaɓa a soyayya da muhimmanci sosai don kara inganta soyayyar su.
Reference
Wannan Rubutu Ba Mallakin Arewanet.com.ng bane!!!
Wannan Rubuta Mallakine ga Shafin Yanar Gizo Ta Masoyabiyu.com
A kiyaye!