ANGWAYE KAWAI::YADDA ZAKA GYARA KANKA KAFUN AURE

 YADDA ZAKA GYARA KANKA KAFUN AURE


Gyaran Jiki Ko Gyaran Kai Ya zama kamar Al'ada aduk lokacin da namiji ko mace zasuyi aure. Wata hanyace da ake neman lafiya amma na jindaÉ—i, wato na abunda ya shafi lafiyar Al'auran Namiji ko Na Mace. 

YAUSHE AKE GYARA JIKI?

Shi dai wannan gyran jiki ana yinshi ne kafun Aure da Kamar Wata ÆŠaya ko biyu ake farashi wasu kuma lokaci baya barinsu domin cimma wannan Gyra na jikin.

Karanta: HANYOYIN DA AKE BI A DAINA ISTIMNA'I (Masturbation)

Wasu Kuma Basu san ma ana yin Gyran jiki kafun Aure ba. Sai bayan sunyi Aure Sun fara samun matsala sannan suke sanin ana gyara jiki kafun Aure.



Karanta: YADDA AKE RAGE SHA'AWA


GYARA JIKI NADA MUHIMMANCI?

Eh Gyara jiki yanada muhimmanci musamman idan aka yishi ta hanyar data dace, batare da an kauce shari'ar musulunci ba, kuma batare da Anyi Abunda Zai illata lafiyar jiki ba.

Karanta: YADDA MATA SUKE KOYON RANGWAÆŠA


TAYA AKE GYARA JIKI?

Wasu Magun Guna ne da Ake haÉ—awa ana shan su kullum, Wasu ana sha Sau É—aya a Rana, wasu sau biyu Har uku ma, ya danganci yanayin Maganin Ne. 

Akasarin Maganin Gyaran Jiki Na Maza Baya wuce itatuwa da Garin Magani Nasha a Kunu Ko a Shayi Ko a Ruwan Sanyi da makamantan su. Wasu kuma maganin ake tafasawa da wasu MahaÉ—ai a ringa sha.

Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA

MEYASA AKE YIN GYARAN JIKI ?

Zamanin Mu ne yazo da wasu abubuwan amfanin yau da kullum kamar su, ZaÆ™i da maiÆ™o, yawan cin Maggi da Kafi, Rashin cin Æ´aÆ´an itatuwa wato (Fruit & Vegetable) wanda WaÉ—annan Sune suke Kashe Gaban ÆŠa namiji ya zama bayada kuzari wajen gamsar da iyali ko mai saurin inzali, ko ƘanÆ™ancewar Gaba, Rashin Samun Ni'ima yayin Jima'i. 

Karanta: YADDA AKE YIN SHAGWABA

Daga Lokacin da mace ta tabbatar Baka gamsar da ita To zata Renaka, sannan zatana maka wasu Halayya na Nuna Maka cewa Auren ka bai kashe mata Sha'awa. Sannan Aure Yana Iya Mutuwa Saboda Rashin Ingancin Maigida ga Iyali. Wannan yasa ake gyara saboda Gudun Matsala.

ABUBUWAN DA SUKE KASHE NAMIJI:

- Yawan Shan Kayan Sanyi

- Yawan Shan Kayan Zaƙi Kamar su Drinks.

- Yawan Cin Indomies.

- Rashin Cin Abubuwan Da jiki ke Buƙata na Kayan marmari.

- Yin Masturvation wato Mutum yayi ta motsa gaban shi. Wanda Hakan Haramun ne ga Musulmi.

- Yawan Cin Mai Da yawa.

- Da Sauran Su.


Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA


WANI LOKACI YA DACE DA GYARAN JIKI?

Lokacin daya dace Da Gyaran Jiki Shine Kafun Aure da Wata Biyu ko Ƙasa da haka kaɗan. Wannan shine zaku samu Isheshshen lokaci domin maganin yayi aiki.

YADDA AKE GYARAN JIKI.

Da zarar Auren ka ya iso daf sai kayi maza ka nemi maganin Gyaran Gida wanda basu wuce Maganin Sanyi Da Basir Ba, Sai Maganin Zaƙi da Maiƙo.

Zaka Iya Samun Waɗannan magunguna a Wurin masu bada maganin Gargajiya Yardaddu, kuma ƙwararru da Suka San Harkar.

Sannan Zaka Iya Zuwa Islamic Medicine Kayi musu Bayani cewa Auren ka ya Matso a HaÉ—a Maka Na Gyaran Jiki. Akwai wasu Magani da zasu HaÉ—a muku Masu kyau, kuma indai kuka daure kuka yi amfani dashi akai Akai Zasu taimaka sosai.

Karanta:ABUBUWAN DAKE BATA SOYAYYA 

YA KAI ANGO SAURA SATI 2 ÆŠAURIN AURE ZAKA FARA WANNAN:

1. A samu cucumber a wanke ta sai asata a blender a markaÉ—e har bawonta idan an markaÉ—e sai a juye a kofi a sa zuma cokali tatacciya sai ka juye ka shanye, zakai haka kullum har ranar É—aurin aure.

2. za'ayi kunun salala na gyaɗa ko gero idan ya dahu an sauƙe sai ka zuba garin habbatulrashad cokali 1 babba ka juye ka shanye shima za'ayi maka kullum har sati 2 zuwa ranar ɗaurin aure.

3. za'a samu albasa manya guda 3 a tafasa sosai sai a sauke ayi blending sai azuba  ruwa da albasar a cakuda sai azuba Zuma a dinga sha, shima Zaka Fara tun saura sati É—aurin aure har zuwa ranar da za'a kaika.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

4. A samu man habbatussauda, man hulba da man RiÉ—i sai a haÉ—esu adinga zuba cokali 1 amadara kanasha har zuwa ranar É—aurin aure.

Zai taimaka maka wajen samum qarfi, kuxari, hana saurin kawowa, yawan ruwan maniyyi, hana gajiya, karsashi da nishadi.


AƘARSHE: ya Kamata lalai maza su tashi tsaye wajen gyara jikinsu kafin aure domin wannan matslaar tana da mutuqar haɗari ga rayuwar aurenmu awanan zamanin domin Mata suna yin Sama da wata 6 suna gyara jikinsu da Shan magani kala kala na sanyi da samun nishadi shiyasa Idan baka gyara ba kana kallon matar zata fi qarfinka bazaka iya da ita ba sai dai kabarta cikin qunci da damuwa daga Haka Kuma tafara samin rauni da damuwa har ta Fara hango wani namijin bakai ba.


ABUBUWAN DA ZAKA KIYAYE.

- Ka Kiyaye Shan Maganin Asibiti Na Ƙara Kuzari ko Riƙe Ruwan Mani. Sunada Illa ga Lafiyar ka dana Iyalinka.

- Kada Kasha Wani Maganin Daba Itace ko Ƴaƴan Itatuwa Ba Da Suna. maganin gyaran gida.

- Ka Guji Baiwa Matarka Magani Muddin baka tabbatar da Ingancin shi ba.

Karanta: YADDA-AKE-GANE-SIFFOFIN-SAMARI-MAYAUDARA

ILLOLIN MAGANIN GYARAN GIDA NA ASIBITI GA LAFIYA:

- Idan Aka fara shan su b'a cika dainawa ba.

- Duk lokacin da ka saba sha su bazaka iya komai ba sai dasu.

- Suna Kawo Yawan Kasala ga Namiji.

-Suna Kawo Mutuwar Gaba.

- Ga Mata Yana Haddasa Musu Matsala a Mahaifa.

- Yana Hana Mace Haihuwa da Kanta sai anyi Mata Tiyata saboda Suna Kashe Ƙarfin Mahaifar Mace yasa ya tsuke.

- Kafun Asha Magani A Tambayi Masani.


Thank you for your message.

Previous Post Next Post