KALMAR INA SON KA A BAKIN MACE YA ZAMA TARIHI A ƘASAR HAUSA!!!
MEYASA??
Mafi yawancin matan Hausawa Sun ƙware wajen ganin sun samu saurayi Irin wanda suke so ko suke Ƙauna. Bayan sun samu daga baya kuma sai su nemeshi su rasa.
Wannan na Faruwa ne Saboda Mazan Hausawa Suma Akwai abunda suke so a wurin matan.
Misali.:
Duk Namijin da Zai Furta Miki Kalmar Ina sonki, tofa Shima Yana son jin Wannar Kalmar ta fito daga Bakin Wacce aka Furtawa domin Shima yaji daɗin data ji.
Karanta:YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE
Amma inaaaaa Matan yanxu Kun Lalace, Ƙalilan Ne daga cikin ku suke iya Haka.
Amma kinsan Cewa Matuƙar kinason Namiji Dole ki Nuna Mishi ta Wurare Kamar Haka:
A Aikace: Wajen Sakar Mishi Fuska, Bashi Kyaututtuka, Mishi Kalamai Masu Dadi.
A boye: Wajen Yawan Ambaton shi Acikin Ƙawaye ko Ƴan Uwa, Dangi da Sauran su.
A Sirrance: Ki Nuna Mishi Wasu Alamu Da Zasu Ɗimautar dashi.
Kamar Tafiya Me kyau a Gabanshi,
Kamar Fari Da Idanu,
Kamar Jefa Mishi Kiss Ta waya ko Cikin Text.
Muddin Kina son Namiji To Sai kin Mishi Irin Abunda Yake miki Kike Jin Daɗi.
Ƴan Mata A Kula Damu Maza, Inba Haka Ba Ayi Kwanan Zaune🥰🖐🏻
Karanta: ABUBUWA GOMA 10 DAKE CUTAR DA MUTUM KULLUM
DAUSAYIN KAUNA
Ma’anar Soyayya
Soyayya wata aba ce da ke shiga cikin zuciya ba tare da ka sani ba kuma ita ce jigon rayuwa.
Alamomin so
Akwai alamomin da ke fitar da so, masu tarin yawa suke bayyana soyayya. Ga kadan daga cikin su:
Kunya: Da zarar soyayya ta fara shiga ko dab’a ayi furuci ba sai kunya ta shiga tsakani, sai a ga masoyan a junansu suna jin kunyar juna.
Yawan Kallo: Wannan alama c eta soyayya, misali ta hanyar yawan satar kallo, idan masoyi yana kallon a bin son shi day a waiga sun hada ido zai kawar da kansa.
Faduwar Gaba: A lokacin da soyayya ta fara shiga zuciyar saurayi ko budurwa za ka samu da zarar sun hango juna kowa sai gabansa ya fadi.
Yawan Ambato: Matukar soyayyar saurayi ta kafu a zuciyar budurwa ko ta budurwa ta shiga ran saurayi, zaka samu yana yawan kawo labarin wanda yake so din ako yaushe, kuma du kina ya ji an fara labarin wanda ya ke son za kaga ya natsu yana sauraro.
Tausayi: Soyayya musamman ta gaskiya tana tare da tausayi. Kuma sau tari zaka ga masoyi ko masoyiya suna matukar tausayi ga junan su, har hakan na haifar da damuwa ko saurin kuka musamman mata.
Har ila yau, Soyayya tana da farillai, da sunnoni, da mustahabbai da sauransu.
FARILLAN SOYAYYA
- Tsoron Allah
- Hakuri
- Rikon Amana
- Kulawa
- Rikon Alkawari
- Fadar Gaskiya
- Tsafta
- Kwalliya
- Kalaman Soyayya
- Kunya
- Kishi
- Iya Magana
- SUNNONIN SOYAYYA
- Zuwa zance
- Kyauta
- Tattali
- Yabawa
- Tarairaya
- Kawar da kai
- Mutunta juna
Karanta: YADDA-AKE-FARA-SOYAYYA-DA-BUDURWA
FA’IDAR YIN AURE DA WURI
Aurar da yara Mata da zarar sun balaga, Ko kuma kafin ma su balaga, yana daga cikin halayen Magabata na kwarai. Kuma yana daga cikin hanyoyin da zamu iya bi awannan zamanin domin dakile barna da ayyukan fasikanci wadanda kullum suke Qara ya’duwa acikin al’ummah.
Ba kamar yadda turawan yamma kullum suke kokarin juyar da tunanin al’ummar Musulmai, suna cewa wai aurar da ‘ya’ya Mata da wuri yana haifar da chututtuka, yana haifar da lalacewar rayuwa da sauran matsaloli kala-kala, wanda kuma duk Qarya ce zalla.
Kuma hujjojin da suke bayarwa akan haka ba karbabbu bane, tunda cututtukan da rashin auren ke haifarwa sunfi girma sunfi muni fiye da duk tunanin mutum.
Yarda da irin wadannan miyagun ra’ayoyin na Turawa yakan sanya wasu daga Jama’ar Musulmai wadanda suke ganin wai kansu ya waye, har suna kallon addininmu da kyawawan al’adunmu kamar wani ci-baya.
Su kansu turawan idan kun duba cikin tarihinsu da tarihin sarakunansu da daulolinsu zaku tarar cewa cike suke da tarihin ‘ya’yan sarakunansu wadanda aka aurar da wuri, har ma suka hayayyafa kuma su turawan suna alfahari dasu.
Karanta: ABUBUWAN-DA-YAKAMATA-KA-SANI-RAYUWA
Hakanan koda acikin Bible dinsu akwai wuraren da suka halatta aurar da yara mata tun suna ‘Yan shekaru biyar-biyar aduniya.
Kuma yanzu haka yaran Turawan Amurka da Ingila da Faransa da sauran Qasashen Turai sukan fara aikata zinace-zinace tun basu fi ‘Yan shekaru sha biyu, sha uku ba. Kafin yarinya ta kai shekaru 20 aduniya ta gama sanin komai tsakaninta da ‘Da Namiji. Kuma su iyayensu basu dauki wannan din abakin komai ba.
Su Turawa a ra’ayinsu Zina ba laifi bane mutukar dai anyita ne bisa soyayya, ko kuma kan ra’ayin masu yinta, ba tilastasu akayi ba. Shi yasa su awajensu aure bashi da wani muhimmancin da za’a kula dashi wajen tsaftace al’ummah.
Amma mu Musulmai awajenmu aure shine jigon rayuwa tunda ta dalilinsa ne ake samun yaduwar al’ummah managarciya. Kuma aure ibadah ne tunda ta hanyarsa ana samun shiga Aljannah. Aure yana tsaftace al’ummah ya hana barna shiga cikinta. Kuma aure yana gyara halayen masu yinsa, ya hanasu afkawa cikin sabon Allah.
Abu ne mai hatsarin gaske a rika Jinkirta ma ‘ya’ya mata da maza yin aure don burin neman abin duniya. Kodai ache wai sai ta gama makaranta ta samu aiki, ko kuma ache ba za’a aurar da ita ga talaka ba. Ana nan ana jiran mai kudi yazo ya aureta Ba’a la’akari da hali ko yanayin da ita yarinyar zata iya shiga saboda sha’awa ko matsuwarta dayin auren.
Wannan duk tsari ne irin na Yahudu da Nasara wadanda mafiya yawansu sukan kare kuruciyarsu ba tare dayin aure ba. Kuma basu kawo tunanin mutuwa azukatansu ballantana suyi tanadi dominta.
Ya zama wajibi iyaye kuji tsoron Allah ku rika bin dokokinsa wajen aurar da ‘Ya’yanku da zarar sun samu Manemi na kirki koda kuwa basu kammala karatun bokon ba. Idan shi Mijin yaso sai su koma suci gaba da karatunsu tare da aurensu. Wanda hakan shine daidai idan ma’aurata sunyi tsari mai kyau. Wannan kuma shine yafi alkhairi da kuma kiyaye tarbiyyarsu daga lalacewa.
Karanta: HANYOYIN-SAMUN-YADDAR-MACE
Ku dubi dai Manzon Allah (saw) duk ‘ya’yansa babu wacce takai shekaru ashirin (20) aduniya kafin yayi aurenta. Ga Sayyiduna Abubakrin Assiddeeq (rta) ya aurar da ‘Yarsa (Nana A’isha) tun tana ‘yar shekaru bkwai (7) aduniya. Kuma ta tare dakin mijinta tana da shekaru tara (9) aduniya.
Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) shima ya aurar da ‘yarsa Ummu Kulsum tun bata kai shekaru 10 aduniya ba. Hakanan Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (ra).
"HAKIKA KYAKKYAWAN ABIN KOYI YA KASANCE GAREKU CIKIN (RAYUWAR) MANZON ALLAH, GA WANDA YAKE QAUNAR ALLAH DA RANAR LAHIRA ".( SURAH AL-AHZAAB).
WANNAN NASIHA CE DAGA ZAUREN