YADDAKE GANE SOYAYYAR GASKIYA

  YADDA AKE GANE SOYAYYAR GASKIYA

Kamar yadda muka saba gabatar muku da shirye shirye da suka shafi Soyayya yau ma, bari na hanga na hango a cikin soyayya akwai abubuwa da dama wadanda idan masoya suka yi amfani da su za su kasance farin ciki har ma ayi ko yi da soyayyarsu.


Kalmar ‘Gaskiya’ a baki akwai saukin fada amma cikin zuciya da kuma a aikace tana da matukar wahala. Idan aka gina soyayya a tubulin karya, komai daren dadewa sai ta ruguje. A wannan lokacin masoya da dama – ban ce duk ba, domin ba duk aka taru aka zama daya ba – amma dai mafiya yawa duk soyayyar karya ce shi ya sa yaudara take shigowa ciki ba ga mazan ba, ba ga matan ba.



 Karanta: YADDA AKE HIRA DA BUDURWA A ONLINE



Saurayi na son mace, ya yi ta feshe ta da kalaman so da kauna, tun ba ta iya rikewa har ta fara haddace kalamansa tsaf; sai ka rantse da Allah duk duniya babu wata ‘ya mace da yake so sama da ita, kuma a zahiri ba haka ba ne; a wasu lokutan za a iya samun yana da ‘yan matan da yake fadawa irin kalaman sama da goma, burinsa kawai a yi soyayya, ba auren ba; ko kuma soyayya don wani abu.

 Karanta: YADDA-AKE-RARRASHIN-BUDURWA


Gaskiya daya ce, idan ka so wata don wani abu nata, wata rana za ka iya rasa wannan abun. Idan ka rasa abin da ya janyo maka soyayyarta shin za ka daina sonta ke nan? Dole ne zuciyarka ta canja a kanta, ka sake kokarin hango wata daban me irin abinda kake so. Ka ga kenan haka za ka dauna cikin hange-hangen da ba zai kare ba, sai ai nazari a yi duba, na san wasu za su halin ai na mata ne ba maza ba, maza ma da nasu domin yanzu su ma sun koya.

Karanta: HOW-TO-MAKE-GIRL-EARGER-TO-SEE-YOU

Ita kuwa budurwa, yayin da ta saka buri a kan lallai sai me wani abu za ta yi soyayyar aure da shi, ranar da ya rasa, shi ke nan an rabu?

To ma, ya za ki kasance idan Allah ya mallaka miki shi a matsayin wanda kika aura, daga baya kuma ya rasa abinda kike so? Dole ne ke ma ki ji canji a zuciyarki. Ga shi kin shiga, yanzu kuma babu damar fita. Haka mace za ta rika tunani a ranta kamar an yaudare ta.

Ba kowa ne yake da irin wannan halin ba; wasu na yi, wasu kuma babu ruwansu da hangen lallai sai me wani abun na kawata duniya, burinsu kawai mai addini, tarbiyya, nutsuwa, kamala, sanin ya kamata da kuma sana’a. Sana’ar ma babu ruwansu da lallai sai wata babba, wadda mace za ta ce ta auri Alhaji wane, su dai burinsu wanda zai iya ciyar da su, shayar da su, tufatar da su, a sauran dawainiya. Ba dauki duinya da zagi ba.

Karanta: YADDA-AKE-KULAWA-DA-SOYAYYA

Har ila yau, babu ruwan da fari, kyakkyawa, dogo (watau irin samarin cikin littafin hausa wadanda ba suda makusa a fagen kyau) duk ba su damu da shi ba. Idan har yana da kyawun hali da dabi’a me kyau da addini, ya wadatar da su, irinsu ba su da yawa a zahiri; jama’a ai duba kuma ai nazari masoya.

Abinda za a rika dubawa a nan shi ne; ya ya tarbiyyar ‘ya’ya za ta kasance bayan an yi aure? Babban burin kowanne mutum nagari ya samu mace ta gari ko ita macen ta samu miji nagari wanda zai tarbiyyantar da ‘ya’yanta wajen dora su turbar gaskiya. Ko kuma shi ya so wadda za ta tarbiyyantar da ‘ya’yansa, idan aka rasa nagari tun daga tubulin soyayya, to lamari ya lalace.

Hange-hange ba zai kari mutum da komai ba face ma bata masa suna da kuma saka damuwa a zuciya.

 karanta: ABUBUWA GOMA 10 DAKE CUTAR DA MUTUM KULLUM?


Babu yadda Allah ba ya ikonSa, idan Ya so sai ya jarabci mutum ma don ya gane imaninsa. Yana da Kyau a rika nazari kafin a aiwatar da wani abu don gudun da na sani. Idan za a so mutum, a so shi don Allah, ba don wani abu nasa ba. A sa cikin zuciya wanda ake so don Allah ake son sa da gaskiya, ba don wata manufa ba.

Idan aka kulla soyayya don Allah to komai zai tafi yadda ya kamata, kuma mutane za su yi farin ciki da wannan son da kuke yi wa juna, har ma a samu wadanda za su yi koyi da su, yawan canje-canje na kawo rugujewar soyayya. Sai a yi duba ai nazari masoya.

Masu Irin wadannan hali sai an mun hakuri, GASKIYA DAYA CE, Hausawa suka ce DAGA KIN TA SAI BATA. Kar a biyewa son zuciya a yi saki reshe kama ganye.

Karanta: YADDA AKE GANE BUDURWA NASON AURE

Ina da abubuwan fada da yawa, amma takaice, a yi soyayya da gaskiya, wadda za ta burge kowa, kuma za ta kai ga aure. Idan mutum ya san ma ba soyayyar gaskiya yakew a abokin soyayyar ba, gwamma kawai ya bari, hakan zai fi zama alheri. Idan yaudara ta shigo ciki abun zai yi ta zama a zuciyar dayan ne wanda kuma yana iya cutar da shi. Sai a duba a yi nazari masoya.

Wannan dan guntun tsokaci ne wanda na yi, da fatan masoya su samu cigaba cikin soyayya ba ci baya ba; ba kuma soyayyar da za ta raba tsakanin masoya ba; ko aboki da aboki; ko kawa da kawa ba; ko soyayyar na gani ina so (Komai ta fanjama fanjam), ba soyayyar ko a mutu Ko a rayu cikin cin amanar masoya ba.

Yana da kyau a yi tunani kafin a aiwatar da komai don gudun fadawa kaidin shedan da kuma yin da na sani wata rana.

Thank you for your message.

Previous Post Next Post